Firay Ministan HKI Banyamin Natanyahu ya bawa kasar Saudiya Shawara samarwa Falasdinawa kasa daga cikin hamada mai girma da take da shi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka wa wata tashar talabijin ta HH a safiyar yau Asabar.
Amma a maida martani ga Natanyahu, dan majalisar dokokin kasar Burtania a jam’iyyar Larbor Afzal Khan yace, wannan shawarar ta Natanyahu tabbaci ne na laifin fitta mutane daga kasarsu da karfi, don kawai ya na son a kwace zirin gaza daga Falasdinawa.
Falasdinawa basa bukatan karin kasa suna son yenci ne a kasarsu. Inji dan majalisar dokoki Kim Johnson na jam’iyyar Lebour..
Kafin haka dai sarki Saman bin Abbdul azizi na kasar Saudiya yace ba zai samar da huldar jakadanci da HKI ba sai an samar da kasar Fal;asdini.