Namibiya : Mace Ta Zama Shugabar Kasa Ta Farko

Namibiya ta zabi shugaba mace ta farko, a tarihin kasar. Netumbo Nandi-Ndaitwah, mai shekaru 72, wace it ace mataimakiyar shugaban kasa a yanzu daga jam’iyya

Namibiya ta zabi shugaba mace ta farko, a tarihin kasar.

Netumbo Nandi-Ndaitwah, mai shekaru 72, wace it ace mataimakiyar shugaban kasa a yanzu daga jam’iyya mai mulki, ta lashe zaben shugabanci kasar kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar da yammacin ranar Talata.

An zabe ta a zagayen farko da kashi 57.31% na jimillar kuri’un da aka kada inji hukumar.

Babban abokin hamayyartsa na jam’iyyar (IPC), Panduleni Itula, mai shekaru 67, ya samu kashi 25.50% na kuri’un da aka kada, saidai ya yi kalubalanci zakamakon zaben.

A jawabinta bayan samun nasarar lashe zaben Netumbo Nandi-Ndaitwah ta yi alkawarin cika alkawuran da ta dauka, musamman samar da ayyukan yi 250,000 cikin shekaru biyar.

A wannan kasa mai mutane miliyan uku, rashin aikin yi ya shafi kusan rabin matasa, bisa ga sabbin alkaluman hukuma na shekarar 2018.

Zababiyar shugabar kasar ta kuma yi alkawarin jawo jarin kasashen waje.

Namibiya, daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da uranium a duniya, kuma ita ce kasa ta biyu da ba ta da daidaito a duniya, a cewar bankin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments