Hedikwatar tsaron Najeriya ta musanta labaren dake yawo na cewa dakarun Faransa na shirin kafa sansaninsu a kasar.
Wata sanarwar da daraktan yada labaran Hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce labaran jita-jita ce, kuma basu da tushe.
Ya ce, “An ankarar da hedikwatar tsaron Najeriya a kan rahotannin da ake yadawa a shafuka sada zumunta da ke zargin cewa zangon farko na dakarun Faransa ya isa Maiduguri a shirye-shirye kafa sansanin su a yanki Arewa maso gabashin Najeriya.
“Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa wannan rahoto na karya ne kuma bashi da makama.
Hedikwatar tsaron ta bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin marasa tushe na son rai.