Najeriya: Kwanaki 62, Iyayen Yan Makaranta Da Yan Ta’adda Suka Sace Suna Jiran Dawowarsu Gida

Kwanaki 62 kenan da garkuwa da yara yan makaranta 42 wanda kungiyoyin yan ta’adda suka sace a jihar Borno na arewa maso gabacin tarayyar Najeriya,

Kwanaki 62 kenan da garkuwa da yara yan makaranta 42 wanda kungiyoyin yan ta’adda suka sace a jihar Borno na arewa maso gabacin tarayyar Najeriya, iyayen suka ce suna jiran lokacinda yaran zasu dawo gidayensu.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa, a ranar 15 ga watan Mayun shekara ta 2026 da muke ciki ne yan ta’adda dauke da makamai suka yi garkuwa da yaran, daga ciki har da yan shekaru 3, 3 a duniya, daga cikin ajunansu a cikin makarantar Mussa a karamar hukumar Askira/Uba na jihar Borno.

A zantawa da jaridar Daily trust ta Najeriya daya daga cikin iyayen, ya bayyana cewa, har yanzun basu san waye ne ya tafi da yayansu ba, saboda basu bada sanarwa ba, kuma ba wanda ya karasu don bayyana masu kudade ko kuma abunda suke bukata don sake masu yayansu ba.

Wani daga cikin iyayen ya ce, tun lokacinda aka sace yarammu bama iya barci sosai, saboda bamu san halin da suke ciki a duk inda aka kaisu ba. Sai dai gwamnatin Jihar Borno ta bada sanarwan cewa ta fadawa wasu iyayen kan cewa tana iya kokarinta don ganin an dawo da yaran hannun iyayensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted