Amurka Ta Kashe Mutane 38 A Harin Da Ta Kai A Iran Kuma Ta Lalata Hasumiyar Tashar Jirgin Ruwa

Rahotanni sun bayyana cewa harin ta’addanci da sojojin Amurka suka kai kan ababen more rayuwar alumma a fadin kasar iran da dare da kuma yau

Rahotanni sun bayyana cewa harin ta’addanci da sojojin Amurka suka kai kan ababen more rayuwar alumma a fadin kasar iran da dare da kuma yau juma’a, sun rusa hasumiyar tashar jirgin ruwa a chabahar kuma sun kashe mutane 8 da kuma jikkata wasu guda 20.

Harin baya bayan nan yazo ne bayan barazanar da shugaban Amurka  trump yayi na cewa zai kai hari kan muhimman wuraren a iran da suka haka da tashohin wutar lantarki da gadoji, adaidai lokacin da majalisar dinkin duniya ta yi shiru kan laifukan yaki da Amurka take aikatawa.

Ministan lafiya na kasar Iran ya sanar cewa a yau jumaa kimanin mutane 38 ne suka mutu yayin da sama da 400 kuma suka jikkata sakamakon harin zalinci da Amurka ta kai .

Ana su bangaren dakarun kare juyin musulunci na kasar iran sun kaddamar da hare hare na mayar da martani kan Amurka, inda suka hari sansaninta da kuma naurorinta dake yankin inda ta harba makamai masu linzami a sansaninta dake kasahen baharain da Kuwait, siriya da kuma kasar Oman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted