Andy Bunham Ya Zama Shugaban Jam’iyar Labour Matakin Karshe Kafin Zaman Fira Minista

Dan majalisar birtaniya mai suna Andy Burnham ya zama sabon shugaban jam’iyar kwadago ta birtaniya mataki na karshe kafin ya zama fira ministan birtaniya na

Dan majalisar birtaniya mai suna Andy Burnham ya zama sabon shugaban jam’iyar kwadago ta birtaniya mataki na karshe kafin ya zama fira ministan birtaniya na 7 a tarihi.

Acikin jawabinsa bayan da aka zabe shi burnham yayi ikirarin cewa gwamnatinsa za ta zama ta labour ce tsantsa, da kuma kula da sabunta tattalin arzki, kara samun iko a kan jamaa da sake farfado da masana’antu da kuma mayar da iko a hannun mutane, musamman ma’aikata a cikin alumomin yankin da jam’iyar labour ta wakilta a gwamnatin biritaniya

Yace muna so mu sake dawo muku da kyakkyawan fata, wannan yanayi ne abin alfahari da kuka bani da iyalai na, kuma na yi alkwarin yaki da jam’iyar masu ra’ayin mazan jiya ta reform party ta Nigel farage.

 Yace muna da hadin kai kuma mun yi amfani da ikon da muke samu daga wannan hadin kai din don yi wa mutane hidima da wuraren wadanda suka dade suna jiran siyasa don su sake samun fata mai kyau,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted