Jamhuriyar Congo ce za ta wakilci Afirka a sauran wasan cike gurbin shiga gasar kofin duniya, bayan da ta yi nasara a kan Najeriya da cin 4-3, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1.
Congo za ta fafata da Bolivia da New Caledonia da Iraki da Jamaica da kuma Panama da za su kece raini a birnin Guadalajara da Monterrey a Mexico a watan Maris.
Super Eagles ta kai gasar kofin duniya shida daga bakwai tsakanin 1994 zuwa 2018, kuma wannan shi ne karon farko da Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo biyu a jere tun 1990, bayan kasa zuwa 2022 a Qatar.
Wannan shi ne karon farko da Congo DR za ta je babbar gasar tamaula ta duniya da zarar ta samu gurbin, bayan 1974 a Jamus, amma a lokacin ana kiranta Zaire.
Za a buga gasar kofin duniya tsakanin tawaga 48 a Amurka da Canada da Mexico a 2026.