Na’im Kassim: Mamaya Tana Da Ranar Da Za Ta Zo Karshe

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi da Imam Hussain ( a.s).

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya gabatar da jawabi a daren jiya a yayin zaman Ashura, ya kuma kara da cewa; tafarkin Imam Hussain ( a.s) shi ne wanda ya samar da gwarazan mazaje na musamman da shahidai da su ka fuskanci ‘yan mamaya.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce;  Matasan da su ka yi watsi da duniya  su ka shiga fagen jihadi, sun sadaukar da kansu.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; kungiyar Hizbullah tana a matsayin kare kai ne,domin wannan kasarmu ce, don haka hakkinmu ne mu kare ta.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted