Na’im Kassim: Kare Kasa Ba Ya Da Bukatuwa Da Izinin Kowa

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim  ya mayar da martani ga wadanda suke son, kungiyar ta mika makamanta, yana mai cewa;

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim  ya mayar da martani ga wadanda suke son, kungiyar ta mika makamanta, yana mai cewa; Ku fara da neman makiya su fice daga cikin Lebanon, domin babu hankali ace ba ku cewa komai akan ‘yan mamaya,ya zamana kuna neman wanda yake gwgawarmaya ya ajiye makamansa.”

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce: Duk wanda ya amince da mika wuya, ya yi, amma mu ba za mu laminta da hakan ba. Mu almajiran makarantar Imam Hussain ( a.s) ne da yake cewa: Ba Za Mu Taba Lamunta Da Kaskanci Ba.”

Sheikh Na’im Kassam ya ce: Wadanda suke jingina da kasashen waje, suna kuskuren lissafi, domin masu gwgawarmaya ba su ganin wani kwarjinin abokan gaba, ba kuma za su sarayar da hakkokinsu ba.”

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa: Babban ci gaba na hakika da aka samu shi ne ‘yanto da kasa, muna kuma cikin Shirin ci gaba da yin haka a kodayaushe.”

Sheikh Na’im Kassim ya jaddada cewa;raya lokacin shahadar Imam Hussain ( a.s),  raya musulunci ne da dukkanin bangarorinsa, da kuma manhajarsa.

 Haka nan kuma ya ce; Musulunci wanda Imam Hussian ( a,s) da iyalan gidansa su ka kare shi, shi ne fidirar mutum tabbatacciya, yana kuna ayyana nauyin da ya rataya akan kowance mutum daidai da gwargwadon dabi’arsa ta namiji ko mace. Nauyin da ya rataya a wuyan namiji shi ne daukar makami domin yin yaki na bayar da kariya, ita kuwa mace ba a dora mata yin hakan ba,amma a lokaci daya abokiyar tarayya ce a cikin jihadi ta hanyar rawar da take takawa a bayan fagen daga, da su ka hada yin tarbiyya da ayyukan da muhimmancinsu bai gaza na namiji a fagen daga ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments