Babban Sakataren Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Na’im Qassem ya bayyana cewa: Amincewa da yin shawarwari da gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma amincewa da sharuddan da wakilin Amurka Tom Barrack ya gabatar ya zama sassauci, yana mai jaddada cewa: Gwamnati tana yin kuskure idan ta bi hanyar sassauci don kawo karshen zalunci kan kasar.
Qassem ya jaddada cewa: Kasar Lebanon, tare da dukkan cibiyoyinta, ita ce ke da alhakin tsara shirye-shirye don tunkarar zaluncin, yana mai jaddada cewa tura sojojin nanayar Isra’ila a yankin kudu da kogin Litani, duk da ci gaba da zalunci kan kasar Lebanon sassauci ne.
Wannan ya zo ne yayin da sojojin mamayar Isra’ila suka sanar a ranar Litinin cewa sun kashe wani dan kungiyar Hezbollah a kudancin Lebanon, a daidai lokacin da ake fargabar barkewar sabon rikici kusan shekara guda bayan tsagaita wuta ta fara aiki.