Shugaban Majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya bayyana cewa, abinda sojojin Isra’ila suke yi, shi ne su shiga gefen wani gari, na wani dan lokaci sanann su gudu, ba su tabbata a wuri daya.
Nabih Barri, ya kara da cewa; Filin daga shi ne wanda yake ayyana makomar abinda zai faru a nan gaba.
Dangane da batun tsagaita wutar yaki kuwa, shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon, ya ce, hankali ba zai yarda da cewa Lebanon zai amince da kudurin da zai kare maslahar Isra’ila da zai cutar da Lebanon da kuma kare huruminta ba.
Nabih Barri ya ce, Matsayarmu a fili take akan tsagaita wutar yaki da kuma aiwatar da kuduri mai lamba 1701.