Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a yau Litinin cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ta kai wa wata mota hari a

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a yau Litinin cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ta kai wa wata mota hari a kusa da garin “Sharqiyya”.

Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon kuwa ya sanar da cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ya jefa bom a kusa da wata motar Buldoza a garin Khayyam, sai dai babu wanda ya jikkata.

Haka nan kuma kamfanin dillancin labarun ya ce; Jirgin saman maras matuki ya jefa wasu bama-baman guda uku akan hanyar Zafta.

A cikin kwanakin bayan na HKI tana kara tsananta kai hare-hare a kudancin Lebanon, lamarin da yake nuni da kokarin sake dawowar yaki gadan-daban.

Tun bayan tsagaita wutar yaki a Lebanon shekarar da ta gabata HKI take keta hurumin kasar ta Lebanon ba tare da kakkautawa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments