Jim Kadan bayan da aka sanar da tsagaita wutar Yaki mutanen Lebanon da su ka zama ‘yan gudun hijira, sun fara koma wa zuwa kauyukansu da garuruwansu.
Su ma mutanen yankin Bikaa’ da unguwar Dhahiya da su ka bar gidajensu saboda yaki,sun fara komawa kasa da sa’a daya bayan da aka fara aiki da hukuncin tsagaita wuta.
Mutanen sun yi watsi da barazanar HKI na cewa kar su koma garuruwan nasu.
A unguwar Dhahiya dake kudancin Beirut, daruruwan mutane sun daga hotunan Sayyid Shahid Hassan Nasrallah da kuma tutocin kungiyar ta Hizbullah. Bugu da kari, mutanen sun rika bayyana farin cikinsu akan cewa sun yi nasara domin Isra’ila ba ta iya kama ko da taku daya na kasar Lebanon ba.
A garin Nabadiyyah ma mazauna garin sun shiga dauke da tutocin Hizbullah da na kungiyar Amal da kuma hotunan Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.
Mutanen Saidah ma sun koma cikin garinsu cikin murna suna dauke da hotunan shahidai da su ka hada da na Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, da kuma tutocin Lebanon, Hizbullah da kungiyar Amal.