Dubun-dubatar al’ummar kasar Aljeriya sun gudanar da wani gagarumin gangami da jerin a wannan Juma’a a birnin Algiers babban birnin kasar, domin yin Allawadai da laifukan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aikatawa a kan al’ummar yankin zirin Gaza.
Kamar yadda kungiyar Movement of Society for Peace ta yi kira, dubban ‘yan kasar Aljeriya ne suka fito domin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu a gaban hedikwatar jam’iyyar da ke unguwar al-Mouradia, babban birnin kasar Aljeriya.
Sai dai hukumomin Aljeriya sun kewaye masu zanga-zangar don hana fadada zanga-zangar zuwa wuraren da jama’a ke taruwa.
Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken nuna rashin amincewarsu da kisan kiyashin da “Isra’ila” ke yi a Gaza, inda suka yi Allah wadai da saka al’ummar Gaza a cikin yunwa da kuma ci gaba da aiwatar da kashe-kashen da Isra’ila ke yi, da nufin tilasta wa al’ummar Palasdinu kauracewa gidajensu da yankunansu . Masu zanga-zangar sun kuma yi kira da a rufe ofishin jakadancin Amurka da ke Aljeriya, saboda rawar da Amurka ta take takawa wajen mara wa Isra’ila baya ga laifukan Isra’ila a Gaza.