Wasu yan bindiga wadanda ake dangantasu da kungiyar Jaishul-Zulum sun dauki alhakin kai hare-hare a cikin wata kotu a birnin Zahidan babban birnin lardin Sistab Baluchistan a yau Asabar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yan ta’addan sun shigo da motarsu har zuwa a wata kotu a garin da Zahidan, sannan suka sauka suna son shiga kotun amma jami’an tsaro a kotun suka hanasu shiga. Daga nan kawai suka fara jefa nakiya irin da yaki a kansu.
An yi ta musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro zuwa wani lokacin suka sami nasarar halakasu. Amma kuma sun kai mutane 6 ga shahada uku daga cikinsu jami’an tsaron kotun da kuma wani yaru da kuma wata mata yar kabilar Baluch wacce har yanzun ba’a ganeta ba.
Kungiyar yan ta’adda ta jaishul Zulum wacce take da cibiya a cikin yankin Baluchistan na kasar Pakisatan dai ta sha daukan alhakin kai hare-hare a yankin Sistan Baluchistan na kasar Iran. Tare da kashe Jami’an tsaro da kuma fararen hula, da kuma kawo hargitsi tsakanin mabiya mazhabobin musulunci daban –daban da kuma kabilu.
Mutane da dama sun ji rauni bayan wadanda suka yi shahada. Sannan mafi yawa an yi masu magani a asbitoci kuma an sallamesu.