Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wani hari a garin “Aytas-sha’ab’ dake kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane biyu.
Kafafen watsa labarun Lebanon sun ambaci cewa, mutanen biyu da su ka yi shahada sun hada da wani makiyayi da dansa da suke kiwon dabbobinsu a burtalin dake kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya.
A jiya Litinin ma dai wani jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniyar, ya kai hari a garin Nabadhiyyah. Har ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan ko harin na jiya ya yi sanadiyyar shahadar wasu ko jikkata. Sai dai kuma gobara ta tashi a cikin motar da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa harin na jiya.
Daga lokacin da HKI ta kai wa kasar Lebanon hari a ranar 8 ga watan Oktoba 2023, mutane da dama sun rasa rayukansu da adadinsu ya kai 4000, sai kuma wasu 17,000 da su ka jikkata. Har ila yau, wasu mutanen Lebanon da sun kai miliyan daya da 400,000 sun yi hijira.
Amma daga lokacin da aka tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Nuwamba HKI ta keta yarjejeniyar sau 3000, ta kuma kashe mutane 209 da jikkata 504,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Anatoli ya ambata.