Murtaniya: Ana Cigaba Da Kidaya Kuri’un Zaben Shugaban Kasa Da Aka Yi

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Murtaniya suna cewa, ana cigaba da kidaya kuri’un da aka kada na zaben shugaban kasar da aka gudaanr a

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Murtaniya suna cewa, ana cigaba da kidaya kuri’un da aka kada na zaben shugaban kasar da aka gudaanr a a jiya Asabar 29 ga watan nan na Yuni.

Masu sanya idanu akan yadda zaben ya gudana sun ce, kaso 40% na wadanda su ka cancanci kada kuri’a ne su ka yi zaben, kuma an gudanar das hi cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban kasa mai ci, Muhammad Ould Ghazouani wanda tsohon soja ne,  yana son a sake zabarsa ne bisa alkawulan da ya yi na tabbatar da tsaro a kasar da cigaban tattalin arziki.

Ghazouani yana fuskantar abokan hamayya su shida, da su ka hada da fitaccen mai fafutukar fada da bauta da kasar ta Murtaniya take fama das hi, da kuma shugabannin jam’iyyun hamayyar siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments