Search
Close this search box.

Mukaddashin Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Kasashen Asiya Su Hada Kai Don Shi Ne Mabudin Samun Karfi

Mukaddashin shugaban kasar Iran Muhammad Mukhbir ya bayyana cewa hadin kasashen Asiya a cikin kungiyar “Asian Cooperation Dialogue ” ko (ADC) shi ne mabudin hadin

Mukaddashin shugaban kasar Iran Muhammad Mukhbir ya bayyana cewa hadin kasashen Asiya a cikin kungiyar “Asian Cooperation Dialogue ” ko (ADC) shi ne mabudin hadin kai da kuma samun karfi a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a taron kungiyar karo na 19 wanda bude a jiya Litinin a nan Tehran, wanda kuma ya sami halattar wakilai daga kasashen Asia fiye da 30.

Labarin ya kara da cewa mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ne ya karanta sakon shugaban kasan a taron na ADC karo na 19 ya kuma kara da cewa, gwamnatin HKI ta kara takurawa falasdinawa a kasar da aka mamaye sai aka samar da kawancen masu gwagwarmaya a yankin don kubutar da kasar Falasdinu daga mamayar yahudawan Sahyoniyya.

Mukhbir ya kara da cewa tarihi ta tabbatar da cewa zalunci ba zai dawwama ba don haka muna daukar kasar Falasdinu a matsayin kasa wacce ba za rabata da sauran kasashen musulmi ba. Kuma kungiyar ADC zata iya taka rawar a zo a gane wajen kawo hadin kai a tsakanin kasashen kungiyar wanda zai maida kasashen yankin a matsayin kasashe masu karfin fada a ji a duniya..

Daga karshe ya ce kasashen yankin zasu shaida kan cewa kasar Iran ta dade tana kokarin kan wannan tafarkin da samar da yankin Asia mai karfi.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments