Kungiyar likitoci marar iyaka ta (MSF, ko Doctors Without Borders) ta ce alamu duk sun nuna cwa Isra’ila na ksian kare dangi a zirin Gaza, kamar yadda Sakatare Janar na kungiyar, Christopher Lockyear, ya bayyana.
M. Lockyear ya kuma fada cewa Isra’ila na nuna “alamomin share wata al’umma a doron kasa ” a hare-haren da sojojinta ke kaiwa a Falasdinu.
Sojojin Isra’ila sun duk wani yanayi na jin dadin rayuwa” a Gaza a watanni 14 na hare-hare kan fararen hula, da wargaza tsarin kiwon lafiya da kayayyakin more rayuwa, da kuma hana taimakon jin kai, in ji kungiyar agaji.
Ya kara da cewa, “Abin da kungiyoyin likitocinmu suka shaida a duk tsawon wannan rikici ya yi daidai da kwatancin da yawan kwararrun masana shari’a da kungiyoyi suka bayar na cwa ana yin kisan kare dangi a Gaza,” in ji shi.
A makon da ya gabata, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri na neman kawo karshen yakin da Isra’ila ta soma tun a watan Oktoban shekarar 2023 a zirin Gaza.
Kasashe 158 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin a ranar 11 ga watan Disamba.
Kudirin ya bukaci “a tsagaita bude wuta cikin gaggawa, ba tare da sharadi ba, kuma na dindindin” a Gaza.
Ko a jiya Alhamis, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta fitar da rahoton cewa Isra’ila ta aikata laifukan kisan kare dangi a Gaza.
Fiye da Falasdinawa 45,100 akasari fararen hula ne ya zuwa yanzu aka kashe tare da jikkata wasu fiye da 107,300 tun bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza.