Moscow: Abubuwan da Isra’ila ke yi a Siriya ya kara ta’azzara halin da ake ciki a kasar

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa: “Ayyukan da Isra’ila ke yi a kasar Siriya ya sabawa sharuddan

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa: “Ayyukan da Isra’ila ke yi a kasar Siriya ya sabawa sharuddan yarjejeniyar Siriya da Isra’ila, kuma yana kara ta’azzara halin da kasar ke ciki.”

Hakan ya zo ne a taron manema labarai da Zakharova ta yi a jiya Laraba, inda ta ci gaba da cewa: “Ayyukan da sojojin Isra’ila suke yi, wadanda suka hada da mamaye yankin Golan da wasu yankuna da ke makwabtaka da su, ya sabawa sharuddan yarjejeniyar Siriya da Isra’ila ta  1974.”

Ta kara da cewa, “Tabbas, kasashen duniya na nuna matukar damuwarsu game da ayyukan da sojojin saman Isra’ila suke yi, da suke kai hare-hare da makamai masu linzami da bama-bamai kan wuraren soji da na fararen hula a yankunan Siriya.”

A cewar Zakharova, Moscow ta yi imanin cewa bisa la’akari da matsanancin yanayi na soji da na siyasa da Siriya ta samu kanta, dukkan kasashen duniya, musamman ma kasashen da ke makwabtaka da ta, suna bukatar  nuna dattako da sanin ya kamata, da kuma daukar matakan da suka dace.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments