Ministocin harkokin wajen kasashen AES na ganawa da Rasha

Ministocin harkokin wajen kasashen kawacen sahel na AES da ya hada Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, na wata ziyarar aiki a kasar Rasha.

Ministocin harkokin wajen kasashen kawacen sahel na AES da ya hada Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, na wata ziyarar aiki a kasar Rasha.

Ana sa ran ministocin za su kasance a birnin Moscow a yau Alhamis da gobe Juma’a, don tattaunawa, da zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, kamar dai yadda aka bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwarsu.

Sanarwar, ta ce shawarwarin da ministocin kasashen kungiyar ta AES za su yi tare da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, wani bangare ne na burin shugabannin kasashen uku na yankin sahel da sojoji ke mulki da kasar Rasha, na fadada hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro.

Har ila yau, sassan biyu za su zanta game da batutuwan da suka shafi moriyarsu, ciki har da samar da daidaito a shiyyarsu, da habaka tattalin arziki da tsaron kasashen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments