Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Ya Zargi “Isra’ila” Da Kokarin Sarrafa Siyasar Kasarsa

Maitamakin shugaban kasar ta Amurka J.D Vance ya bayyana haka ne a hirar da Joe Rogan ya yi da shi, wacce aka watsa a shirinsa

Mataimakin Shugaban Amurka Ya Ce A Shirye Suke Domin Tattaunawa Da Iran

Maitamakin shugaban kasar ta Amurka J.D Vance ya bayyana haka ne a hirar da Joe Rogan ya yi da shi, wacce aka watsa a shirinsa na “Podcast” ya kuma ce; Da akwai alaka a tsakanin Jaffery Estein da kuma kungiyar leken asirin “Isra’ila”.

Bugu da kari Vance ya ce, Isra’ila ta bayar da kudade domin yin parpagandar bata da bakanta yarjejeniya da Iran, kuma shi kanshi Vance yana cikin wadanda ake batawa sunan.”

Vance ya ce; Babu shakku akan cewa da akwai wasu mutane a cikin gwamnatin Isra’ila wadanda suke wasa da ra’ayin mutanen Amurka, suna kuma son karkata siyasar Amurka ta zama ta yaki da Iran ba tare da lokacin karewa ba,maimakon a sami mafita ta diplomasiyya.

Bugu da kari Vance ya ce ‘ A halin yanzu Isra’ila tana rasa masu goyon bayanta a cikin Amurka, wannan kuma abu ne da yake a fili,musamman idan an yi dubi a tsakanin matasa da wadanda shekarunsu su ka haura 65.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted