Ministocin harkokin Masar da Tunisia sun tattauna batutuwan Gaza, Libya, da Sudan

Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya tattauna da takwaransa na Tunisiya Mohamed Ali Nafti kan batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas

Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya tattauna da takwaransa na Tunisiya Mohamed Ali Nafti kan batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya a gefen taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Dangane da ci gaban da halin da ake ciki a Gaza, Abdel Aty ya gabatar da kokarin Masar tare da hadin gwiwar bangarorin shiyya da na kasa da kasa, na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta ba da tabbacin sako mutanen da aka yi garkuwa da su da fursunoni da kuma bude hanyar shigar da kayan agaji. Ya lura da matsaloli na  jin kai da suka biyo bayan manufofin Isra’ila na haifar da yunwa da gangan a yankin.

Dangane da halin da ake ciki a kasar Libya, ministocin biyu sun jaddada muhimmancin tallafawa tsarin siyasar Libya, da janyewar sojojin haya da na kasashen waje, da kuma ci gaba da aiwatar da tsarin sassa uku na kasashen dake makwabtaka da Libya.

A cikin wannan yanayi, ministan na Masar ya yi maraba da sanarwar da manzon musamman na babban magatakardar MDD ya bayar game da taswirar warware rikicin kasar Libya, musamman dangane da batun kafa gwamnatin wucin gadi da za ta shirya gudanar da zabukan kasa a kasar Libya cikin wa’adin watanni 12 zuwa 18.

Bangarorin biyu sun kuma tattauna batutuwan da suke faruwa a Sudan, inda Abdel Aty ya jaddada matsayar Masar na goyon bayan hadin kan kasar Sudan, da ‘yancin kanta, da kuma kudurinta na tallafawa hukumomin kasar Sudan. A cikin wannan yanayi, ya tabbatar da cewa Masar a shirye take ta shiga shirye-shirye da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take da kuma kawo karshen matsalolin jin kai da al’ummar Sudan suke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted