Ministan Leken Asiri Na Iran Ya Yi Karin Bayani Kan Nasarar Samun Bayanan Tsaron HKI

Ministan leken asiri na kasar Iran ya ce asiran tsaron HKI da suka shiga hannun ma’aikatansa sun shafi makaman nukliya na HKI kuma sun nuna

Ministan leken asiri na kasar Iran ya ce asiran tsaron HKI da suka shiga hannun ma’aikatansa sun shafi makaman nukliya na HKI kuma sun nuna kwarewar da jami’an leken asirin kasar suke da shi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan bayanan zasu taimakawa sojojin JMI wajen sanin wuraren da zasu kai hare hare a duk lokacinda yake ya barke tsakanin Iran da haramtacciyar kasar, na makamai da kuma na yanar gizo.

Labarin ya kara da cewa  da jami’an ma’aikatar hukumar leken asiri suka yi kama daga daukar ma’aikatan da suka dace da yin hakan da dabar barun da suke yi amfani da su don kaiwa da bayan da suke bukata ya nuna irin koreawarsu a wannan aikin.

Sannan daga cikin muhimman bayanan da suka samu sun hada da na makaman nukliyar haramtacciyar kasar da kuma dangantakanta da Amurka da kuma kasashen turai rawar da wadan nan kasashe suka taka a karfafa HKI kan makamanta na kissan kaere dangi.

Ministan ya kammala da cewa bayanan da muka samu suna da muhimmanci haka ma hanyar da muka bi muka kai ga bayanan suna da muhimmanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments