Iran Misali Ce Ga Kasashenmu Na Afrika _Ministan Kasuwanci Na Nijar

Ministan kasuwanci da masana’antu na Nijar Malam Seidou Asman, ya ziyarci Iran, inda ya halarci taron Iran da kasashen Afrika karo na biyu da aka

Ministan kasuwanci da masana’antu na Nijar Malam Seidou Asman, ya ziyarci Iran, inda ya halarci taron Iran da kasashen Afrika karo na biyu da aka bude a ranar 26 ga watan Afrilu.

Ya kuma samu halartar taron baje koli na shekara-shekara mai taken (Iran Expo2024) da ya kawo karshe a ranar 1 ga watan Mayun 2024.

”A wani mataki ne na karfafa dangantaka tsakanin Nijar da Iran, Shugaban Majalisar Ceton Kasa ta CNSP, ya tura ministan kasuwanci da masana’antu na kasar ta Nijar domin harlartar wannan taron”.

Malam Seidou Asman, ya gode wa hukumomin Iran game da kyakyawan tarben da ya samu, da kuma gayatar da akayi wa kasarsa a wannan taron na Iran da kasashen Afrika karo na biyu.

A wata tattaunawa ta musamman da tashar HausaTV, ta Iran, ministan kasuwancin da masana’antu na Nijar, ya yaba da yadda mahukuntan Iran ke kokarin karfafa alakarsu da kasashen Afrika.

A daya bangaren kuma ministan kasuwancin da masana’antu na Nijar, ya ce abinda suka gani yayin wannan ziyara a iran, ya sabawa abubuwan da ake fadi game da ita wannan kasa.

Ministan Ya yaba da ci gaban da Iran ta samu a fagage da dama, musamman a irin kayayakin da iran ke kerawa domin kaucewa takunkuman da aka kakaba mata.

A game da yarjejeniyoyin da bangarorin suka cimma kwanan baya, Malam Seidou Asman, ya yi fatan ganin an aiwatar da wadanan yarjeniyoyin domin amfanin juna.

”Yau iran ta zama abun koyi ga kasashenmu wadanda suke da dimbim arzikin iri daban daban, kama daga na karkashin kasa da ruwa, da filayen noma da kiwo da sha’anin kiwon lafiya.

Muna fatan karfafa alaka ta wadannan bangarorin domin dogaro da kan mu inji ministan kasuwanci da masana’antu na Nijar Saidou Asman a tattaunawarsa da tashar HausaTV.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments