A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington.
M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta.
“Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.”
Bayanin hakan ya biyo bayan rahoton da kafar yada labaran Amurka Axios ta bayar cewa, ranar Lahadi ne ake sa ran za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawar tsakanin Iran da Amurka a birnin Muscat na kasar Omani.
Tun da farko dai an shirya gudanar da taron ne a ranar 3 ga watan Mayu, amma aka dage.