Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin.
A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ministocin kasashen tekun Indiya karo na 8 a birnin Muscat na kasar Oman a yau Lahadi, Araqchi ya ce: A yau mun hadu a kasar da aka sani tsawon shekaru aru-aru a matsayin gada da ta hada tsakanin gabas da yamma, kuma tsakanin manyan wayewa da al’ummomi na kusa da na nesa.
Ya kara da cewa: Kasar Oman, mai masaukin bakin al’adu, ba kawai ta kasance a tsawon lokaci tana taka rawa ba ce a fannin tattalin arziki, har ma ta kasance wata alama ce ta taimakekkeniya da tattaunawa da diflomasiyya mai ma’ana a yankin tekun Indiya, wanda a ko da yaushe ke kan gaba wajen ci gaban duniya, mai taka muhimmiyar rawa a makomar tattalin arzikin kasa da kasa.
Ministan harkokin wajen ya kara da cewa: A tsawon tarihi, tekuna sun kasance tamkar kofofin da suke hada tsakanin wayewa, ba iyakokin kasa ba tsawon dubban shekaru, tekun Indiya ba ruwa ne kawai, har ma ya kasance babbar hanyar kasuwanci, musayar al’adu da ci gaban wayewa. Wannan hanya ta hada ‘yan kasuwa daga gabar tekun Indiya zuwa Afirka, daga tsibiran Indonesiya zuwa Tekun Fasha, da kuma daga Iran zuwa Tekun Bahar Maliya. A lokacin da hanyoyin kasa suke da tsawo kuma ba su da aminci, teku ce ta hada kasashe masu tasowa da kuma samar da sabbin damammaki.