Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da ke ziyara a Qatar ya gana da shugabannin Hamas a inda suka tattauna batun sake gina Gaza.
Tattaunawar a birnin Doha ta hada fitattun jami’an kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da suka hada da Mohammed Darwish shugaban majalisar tuntuba ta Shura da Khalil al-Hayya babban mai shiga tsakani na kungiyar.
A yayin ganawar, Darwish ya bayyana Operation Al-Aqsa Storm a matsayin wani sabon salo a gwagwarmayar da al’ummar Palastinu ke yi da gwamnatin mamaya.
Ya jaddada cewa yunkurin gwamnatin Isra’ila na raba al’ummar Falasdinu da kasarsu ta hanyar yakin kisan kare dangi da sauran hanyoyi ya ci tura.
Ya nanata cewa al’ummar Falastinu sun ci gaba da dagewa wajen kare hakkinsu da kuma wurare masu tsarki na kasarsu ciki har da masallacin Al-Aqsa.
A nasa banagre ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya jaddada irin goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take ba wa gwagwarmayar al’ummar Palastinu, sannan ya yaba da irin jaruntakar da al’ummar Gaza suka yi, lamarin da ya ce ya tona a fili gazawar gwamnatin Isra’ila.