Ministan Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ya Bukaci Su Mamaye Yankin Arewacin Gaza

Wani ministan a gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yayi kira ga fira ministan gwamnatin Isra’ila da ta mamaye arewacin Gaza ya zame mallakin yahudawan sahayoniyya Ministan

Wani ministan a gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yayi kira ga fira ministan gwamnatin Isra’ila da ta mamaye arewacin Gaza ya zame mallakin yahudawan sahayoniyya

Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich mai tsaurin ra’ayin sahayoniyanci ya jaddada yin kira ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya mamaye arewacin Zirin Gaza domin ya zame mallakin yahudawan sahayoniyya.

A yayin taron wata makarantar addini ta yahudawan sahayoniyya, ministan kundin Smotrich ya ce: Dole ne yahudawan sahayoniyya su dauki matakin mamaye arewacin Zirin Gaza, kuma su jaddada wa kungiyar Hamas cewa idan ba ta ‘yantar da fursunonin yahudawan da ta kama ba, to lallai za ta yi hasarar kashi uku na yankin Zirin, yana mai jaddada cewa: Kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ga falasdinawa ba zai ƙare ba har sai sun kawar da kungiyar Hamas gaba ɗaya kuma sun tabbatar da ‘yancin yin abin da suka ga dama a Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments