A kasar Iraki,miliyoyin mutane sun cika birnin Karbala domin yin juyayin shahadar Ahlul Bayti ( a.s), a tsakanin hubbaren Imam Hussain da dan’uwansa Abul Fadal Abbas ( a.s).
Masoya Ahlul Bayti ( a s.) da su ka fito daga cikin kasar ta Iraki da kuma wasu kasashe, sun yi cincirindo a cikin birnin na Karbala a tsakanin hubbaren Imam Hussain da Abul Fadal Abbas ( a.s).
Cibiyar da take kula da wuraren masu tsarki a Karbala ta yi tsari na kula a tafiyar da juyayin a cikin tsaro da kuma gabatar da hidima ga masu Ziyara.
An girke jami’an tsaro masu tsaro yawa a cikin birnin na Karbala da zagayen haramin Imam Hussain ( a.s) , haka nan kuma an girke na’urorin gano abubuwa masu fashewa a wurare mabanbanta da su ka hada da mashiga hudu ta garin.