Miliyoyin al’umma daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da jerin gwanon zagayowar ranar Kuds ta duniya wacce ta gudana yau.
An dai kebance ranar ce domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu, kuma ana gudanar da ita ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan ramadana bisa fatawar jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Khumeiny.
A Iran ma kamar sauren sassan duniya jama’a sun fito kan tituna domin gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya, inda suke bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa tare da yin tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza.
An kuma yi irin wannan gangamin a kasashe da dama na yankin yammacin Asiya da suka hada da Iraki da Yemen da Lebanon da kuma wasu da dama a fadin duniya.