Kasashe mambobin kungiyar BRICS na kasashe masu tasowa sun jajirce wajen kokarin kawar da dalar Amurka a harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani ne ya bayyana hakan a jiya Asabar yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen taron tattalin arzikin kasa da kasa karo na 15 na “Rasha-Islamic World: KazanForum 2024” a birnin Kazan na Jamhuriyar Tatarstan.
Ya ce mambobin BRICS sun kuduri aniyar rage dogaro da dalar Amurka amma suna bukatar samar da ababen more rayuwa a fannoni daban-daban domin ganin hakan ya tabbata.
Ya kara da cewa kwararu na kasashen BRICS na gudanar da tuntubar juna akai-akai don samar da hanyoyin cimma manufar rage tasirin dalar Amurka.
BRICS ta ƙunshi Brazil, Rasha, Indiya, Sin, da Afirka ta Kudu. Kasashen kungiyar ne ke da kashi 42 cikin 100 na yawan al’ummar duniya.
Kungiyar dai ta kara zama mai matukar muhimmanci wajen tunkarar al’amuran kasa da kasa tun bayan kafuwarta a shekara ta 2006, kuma ana kallonta a matsayin mai cin karo da karfin siyasa da tattalin arzikin kasashen yammacin duniya.