MDD: Yunwa Ta Kara Tsanani A Duniya Daga Shekarar 2024

A wani rahoton da MDD ta fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa, tun daga 2024 ne yunwar da ake fuskanta a duniya ta

A wani rahoton da MDD ta fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa, tun daga 2024 ne yunwar da ake fuskanta a duniya ta kara tsanani domin ta shafi mutanen da sun kai miliyan 295.

Rahoton  ya kara da cewa; wannan adadin na mutanen dake fama da yunwa mai tsanani suna warwatse a cikin kasashe 53 na duniya.

A  Juma’ar da ta gabata aka fitar da wannan rahoton. Haka nan kuma an bayyana cewa idan aka kwatanta da yunwar da aka yi fama da ita a shekarar 2023, to da aka shiga 2024 an sami karuwar masu fama da matsananciyar yunwar da adadinsu ya karu da  miliyan 13.7. Shekaru shida kenan a jere da ake samun karuwar yawan mutanen da suke fama da yunwa.

An kaddamar da wannan rahoton ne a karkashin kawancen kasa da kasa na fada da karancin abinci a duniya wanda ake kira da ( GNAFC) wanda ya kunshi hukumar Abinci ta duniya ( FAO), da kuma ( WFP) da sauran kungiyoyin da ba na gwamnati ba.

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana alkaluman da aka fitar na adadin masu fama da matsananciyar yuwa da cewa; Wani adadi ne wanda bai girgiza duniya ba, domin tana tafiya ne a karkace.”

Wani sashe na rahoton ya yi ishara da cewa da akwai dalilai masu yawa da su ka haddasa  karancin abinci; sun kuwa hada da talauci, koma bayan tattalin arziki, sauyin yanayi mai tsanani, sai dai kuma duk da haka rikice-rikice da fadace-fadace a cikin wasu yankuna, su ne ummul-haba’isin karancin abincin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted