MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
Hukumar kare hakkin bil’adam dake karkashin MDD ya sanar da cewa tana sa ido akan kashe-kashe da rashin adalcin da ake yi a karkashin zaben
Hukumar kare hakkin bil’adam dake karkashin MDD ya sanar da cewa tana sa ido akan kashe-kashe da rashin adalcin da ake yi a karkashin zaben shugaban kas ana kasar Tanzania.
Tun a ranar Larabar da ta gabata ne dai da ake zaben rikici ya barke a kasar saboda kin amincewar ‘yan hamayya akan yadda zaben zai gudana ba tare da manyan ‘yan takara ba. Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan ce dai babbar ‘yar takara.
Babbar jam’iyyar adawa ta sanar da cewa fiye da mutane 700 ne aka kashe a fadin kasar da ake Zanga-zanga.
Shugaban ofishin hukumar kare hakkin bil’adama na MDD Seif Magango ya sanar da cewa; Sun karbi rahoranni daga majiya mai tushe akan cewa a kalla an kashe mutane 10.
Hukumar ta yi kira ga jami’an tsaron kasar ta Tanzania da su daina amfani da karfi a inda bai dace ba, daga cikin har da amfani da makamai akan masu Zanga-zanga. Haka nan kuma sun yi kira ga masu Zanga-zanga da su yi a cikin ruwan sanyi.
Ita kuwa kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta ce nata rahoton ya tabbatar mata da cewa an kashe abinda bai kasa mutane 100 ba.
Tuni dai aka kafa dokar ta baci da hana zirga-zarga a babban birnin ksar Darus-salam, ana kuma rufe hanyoyin sadarwa na interten daga lokaci zuwa lokaci.
Har ila yau MDD tana yin kira da a saki dukkanin wadanda ake tsare da su.