MDD Tace Yara Kimani 660,000 Ne Aka Hanawa Karatu A Gaza

Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar

Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya tura a shafinsa na X a ranar Litinin.

Ya kuma kara da cewa, ba yadda wadannan yara zasu je makaranta saboda yakin, babu makarantun da zasu shiga don HKI ta rusa mafi yawan makarantu a gaza, sannan ta kashe da dama daga cikin malaman makarantun a yankin.

Lazzarini ya yake nanata bukatar a tsagaita budewa juna wuta saboda yara a gaza su sami damar zuwa makaranta kamar sauran  tokwarorinsu a Duniya.

Hukumar UNRWA ta bayyana cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata ya bada sanarwan cewa HKI ta rusa kashe 97 % na makarantun gaza. Ta kuma kara da cewa kashi 92 na gine-ginen makarantu, wato a cikin makarantu 564 an rusa 518. daga cikinsu. Wasun sun lalace ta yadda sai dai a sake gina nasu tun farko.

Hukumar daga karshe ta bayyana cewa a halin yanzu bata da abinda zatawa yiwa Falasdinawa, duk tare da cewa ta dauki shekaru tana kula da falasdinawa yan gudun hijira tun bayan kafa hukumar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments