MDD ta yi gargadi game da tabarbarewar al’amuran jin kai a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargaba kan yadda ake ci gaba da samun karuwar matsalar jin kai a zirin Gaza, inda ta bayar da rahoton

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargaba kan yadda ake ci gaba da samun karuwar matsalar jin kai a zirin Gaza, inda ta bayar da rahoton cewa akalla Falasdinawa 142,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin mako guda kacal saboda tsanantar hare-haren bama-bamai na Isra’ila.

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a wani taron manema labarai a jiya Laraba cewa, hare-haren da kuma umarnin gudun hijira, tare da hana kayan da ke shiga Gaza da kuma hana ayyukan jin kai a cikin yankin, suna yin mummunan tasiri ga daukacin al’ummar sama da miliyan biyu.

Dujarric ya yi nuni da cewa, yayin da rikicin ya tsananta, ana sa ran adadin mutanen da suka rasa matsugunansu zai karu sosai.

A yammacin ranar Talata, OCHA ta yi gargadin cewa mutane da yawa a yanzu “suna zaune a kan tituna, suna cikin tsananin bukatar abinci, ruwan sha.”

A ranar Laraba an kashe fiye da mutane 39 tare da jikkata wasu 124 cikin sa’o’i 24 sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments