Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun yi gargadi a jiya Laraba cewa, miliyoyin mutane a yankuna akalla 12 da ke fuskantar rikici a duniya, ciki har da Sudan da zirin Gaza, na fuskantar barazanar yunwa, tare da gabatar da bukatar gaggawa na samar da kudade don magance gibin tallafin abinci, sakamakon raguwar tallafin da kasashen duniya ke bayarwa.
A cikin wani rahoto na hadin gwiwa, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) sun sanya kasashen Haiti, Mali, Sudan ta Kudu, da Yemen cikin kasashen da ke fuskantar barazanar yunwa.
Rahoton ya kuma bayyana halin da ake ciki na yunwa a wasu kasashe shida wato Afganistan, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Myanmar, Najeriya, Somaliya, da Syria, a matsayin mai matukar tayar da hankali.
Kungiyoyin biyu sun yi gargadin cewa rashin samun kudade na agajin jin kai na nuni ne Babbar matsalar da za a iya matukar dai ba a dauki matakan gaggawa ba.
Hukumar samar da abinci ta duniya da FAO sun yi kira da a kara samar da n tallafi daga gwamnatoci da masu hannu da shuni, tare da lura cewa kudaden da aka samu har zuwa karshen watan Oktoba sun kai dala biliyan 10.5 ne daga cikin dala biliyan 29 da ake bukata domin taimakawa masu fama da matsaloli irin wadannan a duniya.
Rahoton ya yi nuni da cewa, Amurka wadda ita ce kasar da ta fi bayar da tallafi ga kungiyoyin biyu a bara, ta rage yawan taimakon da take ba wa kasashen waje karkashin jagorancin shugaba Donald Trump, sannan wasu manyan kasashe ma sun rage ayyukan ci gaba da taimakon jin kai, ko kuma sun bayyana aniyarsu ta rage yawan taimakon da suke bayarwa.