MDD Ta Yi Gargadi Akan Tsanantar Yunwa A Kasar Sudan

A jiya Laraba ne dai Hukumar da take kula da harkokin jin kai dake karkashin MDD  ( OCHA) ta bayyana cewa; Kusan shekaru biyu na

A jiya Laraba ne dai Hukumar da take kula da harkokin jin kai dake karkashin MDD  ( OCHA) ta bayyana cewa; Kusan shekaru biyu na yakin da ake yi a Sudan ya kara tsananta, kuma a halin yanzu yunwa wani abu ne da ya zama dahir ana ganinta a kasa a Sudan.

Babbar daraktan  gudanar da ayyukan hukumar agajin ta MDD Edem Wosornu ta fadawa kwamitin tsaron MDD cewa; Da akwai mutane miliyan 12 da aka tarwasta daga gidajensu, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3.4 da su ka tsallaka iyaka. Haka nan kuma fiye da rabin mutanen kasar Miliyan 24.6 suna fama da matsananciyar yunwa.”

Haka nan kuma ta kara da cewa; Tsarin kiwon lafiya na kasar ya durkushe baki daya, da akwai miliyoyin kananan yara da su ka daina karatu, wasu kuma an ci zarafinsu.”

Bugu da kari, saboda fadan da ake ci gaba da yi, an dakatar da kai kayan agaji zuwa sansanin ‘yan hijira mafi girma na Zamzam, alhali suna da bukatuwa da agajin.

A ranar Litinin da ta gabata ne dai kungiyar likitoci ba tare da iyaka ba        ( Médecins Sans Frontières )  ta nuna rashin jin dadinta da yadda rashin tsaro ya tilasata ta dakata da ayyukanta a sansanin Zamzam.

Jakadan Sudan A MDD Al-Harith Idriss ya ce, kasarsa a shirye take ta samar da yanayin da zai bayar da damar ci gaba da gudanar da ayyukan agaji a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments