Kungiyar M 23 mai samun goyon bayan Rwanda ta kara samun gindin zama a gabashin kasar DRC, duk da cewa ta sanar da tsagaita wutar yaki ta gefe daya a jiya Laraba.
Mayakan na M 23 sun sanar da kame babban binin gundumar Bukavu.
Wani jami’in MDD wanda ya isa garin Goma ya bayyana cewa, Da akwai yiyuwar barkewar wani sabon rikici.
MDD ta ce har yanzu ana ci gaba da yaki tsakanin sojojin gwamnati da kuma mayakin na kungiyar M 23.
Garin Goma da mayakan na M 23 su ka kwace iko da shi, yana da ma’adanai kwance a kasansa da aka yi kirdadon cewa kudadensa sun kai na biliyoyin daloli.