MDD Ta Sake Yin Kira Ga Isra’ila Da Ta Janye Daga Tuddan Golan Na Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta sake yin kira ga Isra’ila da ta janye daga tuddan Golan na kasar Siriya, wanda ta mamaye tun bayan yakin 1967.

Majalisar Dinkin Duniya ta sake yin kira ga Isra’ila da ta janye daga tuddan Golan na kasar Siriya, wanda ta mamaye tun bayan yakin 1967.

Kudurin da aka zartar a ranar Talata ya sake tabbatar da rashin amincewar mallakar yankin da karfin tsiya, kuma an amince da shi da kuri’u 97, sannan 8 suka ki kada kuri’a, yayin da 64 suka ki amincewa.

Kudurin wanda wasu gungun kasashe da suka hada da Bolivia, Cuba, Koriya ta Arewa, da wasu kasashen Larabawa suka gabatar, ya jaddada cewa dole ne Isra’ila ta janye zuwa kan iyakokin da ke gabanin shekara ta 1967, daidai da kudurin kwamitin sulhu na MDD.

Har ila yau, ta ayyana sanya dokar da Isra’ila ta yi kan tuddan Golan a matsayin “marasa amfani.”

Takardar ta yi Allah wadai da ci gaba da mamayar da Isra’ila ke yi a yankin, inda ta bayyana haramcin ayyukan matsugunan da sauran ayyukan Isra’ila tun daga shekara ta 1967.

Haka zalika takardar ta jaddada cewa mamayar na ci gaba da zama wani babban cikas ga samar da adalci, da dauwamammen zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Kudirin ya kuma bukaci da a sake gudanar da shawarwarin zaman lafiya a bangarorin Syria da na Lebanon, inda ya bukaci kasashen duniya da manyan bangarori da su farfado da shawarwarin da aka yi bisa kudurin kwamitin sulhu mai lamba 242 da 338.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments