Babban magatakardar MDD Antonio Gutrres ya kira yi HKI da ta dakatar da hare-haren da take kai wa Syria da hakan yake a matsayin keta hurumin wannan kasa.
Babban magatakardar MDD ya bukaci ganin Isra’ilan ta yi aiki da tsagaita wutar yaki da aka yi a 1974 a tsakaninta da Syria.
A gefe daya babban magatakardar MDD ya yi ishara da halin da ake ciki a kasar ta Syria da mutane suke da bukatuwa da kayan agaji, tare da cewa a yanzu sun mayar da hankalinsu akan wannan batu.
Har ila yau babban magatakardar MDD ya ayyana wata lauya ‘yar kasar Mexico Karl Quintana a matsayin wacce za ya kula da batun gano wadanda su ka bace a kasar Syria. Gutrres ya kuma bukaci ganin an bai wa Quintana damar shiga kowane lungo da sake a cikin kasar ta Syria domin gudanar da aikinsu.
Tun bayan da masu dauke da makamai su ka kawo karshen gwamnatin Basshar Asad ne a ranar 27 ga watan Nuwamba na wannan shekarar mai karewa, HKI take kai wa Syria hare-hare da kuma mamaye wasu yankunan mabanbanta na kasar da su ka hada da tuddan Gulan.