Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar DD , ta amince da kudirin dokar da ta yi Allah wadai da yadda dakarun RSF ke kara kai hare-hare a al-Obeid da ke Sudan, inda ta kafa kwamitin binciken gaggawa kan zargin cin zarafin da ake aikatawa a yankin.
Birtaniya tare da wasu ƙasashe 14 ne dai suka gabatar da kudirin, inda suka yi gargadin cewa akwai yiwuwar dakarun RSF sun aikata manyan laifuka, a lokacin kwace iko da birnin al-Fashir da ke Darfur ta Arewa a bara.
Shima wakilin kasar Afrika ta Kudu Zaheer Laher ya goyi bayan kudirin, inda ya bukaci gaggauta daukar mataki akan lamarin,a dai-dai lokacin da RSF ke sake amfani da salon kisan kare dangi da suka yi amfani da shi a al-Fashir.
A baya dai RSF ta sha musanta irin wadannan zarge-zargen cin zarafin da ake mata, a yakin da suka kwashe sama da shekaru 3 su na yi da dakarun kasar, ta na mai cewa abokan gabansu ne ke kirkirar labaran karya da kuma tuhume-tuhume a kansu.