MDD ta goyon bayan kafa kasar Falasdinu da gagarimin rinjaye

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da “Sanarwar New York” da nufin farfado da shawarwarin samar da kasashe biyu a Gabas

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da “Sanarwar New York” da nufin farfado da shawarwarin samar da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya  wato Isra’ila, da kuma Falasdinu a daya bangare – amma ba tare da kungiyar Hamas ba.

Kasashe 142 ne suka amince da shi, yayin da 10 suka nuna adawa da shi (ciki har da Isra’ila da Amurka) sai 12 da suka kaurace kada kuri’ar. .

Bayan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, kasashe da dama sun bayyana aniyarsu ta daukar irin wannan matakin a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a bude ranar 22 ga watan Satumba, ana kallon wannan tsari a matsayin karin tursaswa Isra’ila ta kawo karshen yakin da take ci gaba da yi a Gaza, tuno bayan harin Hamas a ranar 7 ga watan Oktoban 2023

Isra’ila ta yi watsi da kudurin da aka amince da shi a zauren na Majalisar Dinkin Duniya, tana mai kallonsa a matsayin karfafa gwiwar Hamas. Wannan “abun kunya ne,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila Oren Marmorstein a shafin X. “

A nata bangare Falasdinu ta bakin mataimakin shugabanta Hussein al-Sheikh ta ce Wannan kuri’ar wani “muhimmin mataki ne na kawo karshen mamaya…

Shi dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fito fili a ranar Alahamis data gabata yana mai cewa: “Ba za a samar da kasar Falasdinu ba,”  kuma dama kafin hakan abokin kawancensa na Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ba za a bar shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya je New York ba domin halartar babban taron MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted