MDD Ta Goyi Bayan Kafa Kasar Falastinu Mai Ci Gashin Kanta

Yayin da take neman gwamnatin sahyoniyawan ta janye daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, Majalisar Dinkin Duniya ta kuma goyi bayan kafa kasar Falasdinu. A

Yayin da take neman gwamnatin sahyoniyawan ta janye daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, Majalisar Dinkin Duniya ta kuma goyi bayan kafa kasar Falasdinu.

A cewar Aljazeera, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da shirinsa na gudanar da taron kasa da kasa a watan Yunin shekarar 2025 domin sake karfafa kokarin da ake yi na samar da kasashe biyu.

Bisa kudurin da kuri’u 157 suka amince da kuma kuri’u 8 na adawa da shi, Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa tana goyon bayan kafa kasashe biyu ba tare da sharadi ba kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

A halin da ake ciki dai Amurka da gwamnatin Sahayoniya na daga cikin masu adawa da kudirin, sai kuma wasu kasashe sun ki kada kuri’a.

Kudirin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne Isra’ila da Falasdinu su zauna tare cikin lumana da tsaro tare da amincewa da iyakokin da suka dogara da kan iyakokin da aka amince da su kafin shekarar 1967.

Don cimma wannan buri, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gudanar da babban taron kasa da kasa a birnin New York a watan Yunin shekarar 2025, wanda Faransa da Saudiyya za su jagoranta, da nufin farfado da yunkurin diflomasiyya na cimma matsaya kan batun samar da  kasashen biyu. .

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi kira da a tabbatar da hakkokin al’ummar Palasdinu, da kuma hakkinsu na cin gashin kai da kuma ‘yancinsu na samun ‘yancin kamar kowace kasa ta duniya.

Har yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya na kallon yankunan Yammacin Gabar Kogin Jordan da Gabashin Kudus da Zirin Gaza a matsayin yankunan da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye ba bisa ka’ida ba.

Wakilin Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya bayyana cewa: Tun bayan kafa wannan kungiya, batun Palastinu yana cikin ajandar Majalisar Dinkin Duniya, kuma har yanzu wannan batu ne ya zama wata babbar jarabawa ga wanann Majalisa domin tabbatar da adalcinta.

Jakadan Australiya a Majalisar Dinkin Duniya James Larsen, ya shaidawa babban zauren taron cewa: “Maganar kafa kasashe biyu ita ce kawai hanyar warware rikici da tashe-tashen hankula marasa iyaka, kuma wannan mafita ita ce fata guda daya tilo na samar da makoma mai inganci ga Falasdinu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments