MDD Ta Ce Hare-Haren HKI Kan Kayakin Tsaro Na Kasar Siriya Keta Hurumin Kasar

Babban sakatren MDD Antonio Gutteres ya yi allawadai da HKI saboda hare-haren da take kaiwa kasar siriya a cikin lokacinda kasar take cikin wani hali

Babban sakatren MDD Antonio Gutteres ya yi allawadai da HKI saboda hare-haren da take kaiwa kasar siriya a cikin lokacinda kasar take cikin wani hali na rashin tabbas.

Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gutteres yana fadar haka a jiya Alhamis. Ya kuma kara da cewa mamayar yankuna wadanda aka ware bayan yarjeniyar shekara ta 1974 bayan yakin shekara ta 1973, sojojin MDD ne kawai suke da damar shiga wurin, don yarjeniya c eta zaman lafiya.

Babban sakatarin ya kara da cewa, kai hare-hare kan makamai na kasar Siriya a cikin wannan halin keta hurumin kasar ne kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Babban sakatarin dai yana maida martani ne ga wata wasika wacce HKI ta mika masa, inda a ciki take bayyana cewa, ta mamaye wasu yanzuna a kusa da tuddan Golan na kasar Siriya ne a takaitaccen lokaci, sannan ta yi haka ne don tabbatar da tsaron kasar,

Ya zuwa yanzu dai sojojin HKI sun kutsa cikin kasar Siriya, sun kuma mamaye tudun Jabal Sheikh inda tana nan sun iya sanya ido kan aabubuwan da suke faruwa a cikin kasar Siriya da kuma kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments