Babban sakantaren MDD António Guterres, ya yi kira ga mabambantan bangarori masu ruwa da tsaki a Yemen da su yi iyakacin kokarin yin hakuri da juna, su kuma dakatar da kowane irin matakin soja, inji kakakinsa a wata sanarwa.
Sanarwar ta ce, “Mun lura da cewa, Amurka ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare dake karkashin ikon ‘dakarun’yan Houthi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kowane matakin soja da za a dauka na iya tsananta halin da ake ciki, zai kuma haifar da mummunan tasiri, tare da gurgunta yanayin kwanciyar hankali a Yemen, kana zai kara kamarin kalubalen halin jin kai a kasar.”
‘Yan Houthi dai sun yi barazanar karin kai hare-hare kan jiragen ruwa dake ratsa tekun maliya”.