Babban zauren MDD ta amince da kudurori guda biyu wadanda suka yi tir da HKI a jiya talata dangane da mamayar da take yiwa kasar Falasdinu tun shekara 1967 da kuma tuddan golan na kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa HKI ta mamaye tuddan golan na kasar Siriya ne tun yakin kwanaki 6 a shekara 1967 sannan gwamnatin HKI ta tabbatar da kwace yankin a shekara ta 1981. Amma kwamatin tsaron MDD ta yi watsi da mamayar tun lokacin, ta bayyana hakan mamaya ne ba bisa ka’ida ba.
Labarin ya kara da cewa, kasashen Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Palestinu ne suka gabatar da kudurin wanda ya sami amincewar kasashe 151, 11 na wadanda basu amince ba (wadanda suka hada da Amurka da HKI) da kuma 11 na wadanda basu kada kuri’arsu ba.
Dangane da tuddan golan kuma wanda kasar Masar ta gabatar, ya sami amincewar kasashe 123, 7 na wadanda basu amince ba sannan 41 na wadanda suka ki kada kuri’unsu. Kudurin da babban zauren ya amince da shi dangane da Falasdinu dai y ana goyon bayan samar da kasashe biyu. Da kuma kira zuwa ga kawo karshen mamayar da HKI take wa kasar Falasdinu tun shekara ta 1967