MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza.

Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar.

Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje na wucin gadi don kula da tsaro, tallafawa sake ginawa da kuma kiyaye tsari a yankin. Daftarin ya yi kira ga rundunar ta yi aiki na tsawon shekaru biyu, tare da yiwuwar kara sabunta wa’adin aikinta wanda ya danganta ne da ci gaban da ake samu a kasa.

Kudurin ya kunshi abubuwa da yawa,  ciki har da kare iyakokin Gaza, kare fararen hula, kare hanyoyin jin kai, da kuma horar da sabbin ‘yan sandan Falasdinu da aka tantance. Hakanan ya ba da izinin amfani da “dukkan matakan da suka wajaba” don cimma wadannan manufofi, gami da wargaza kungiyoyi masu dauke da makamai da kwace makamai marasa lasisi.

Muhimmin fasali na kudurin shine ƙirƙirar hukumar wucin gadi, wacce wani lokacin ake kira “Hukumar Zaman Lafiya,” wacce za ta yi aiki tare da rundunar kasa da kasa don taimakawa wajen gudanar da harkokin Gaza. Shirin ya kuma yi kira da a shigar da cibiyoyin kuɗi na duniya, kamar Bankin Duniya, don ba da kuɗaɗen ayyukan sake ginawa da kuma kula da gudanar da asusun tallafi na musamman.

Daftarin kudurin ya jawo suka daga ƙungiyoyin Falasɗinawa, waɗanda ke bayayya cewa ya ƙunshi wani nau’i na mulkin mallaka da Rashin ‘yancin kai, daga cikin kungyoyin da suka nuna damuwa kan kudirin har da kungiyar Hamas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments