MDD ta bayyana cewa; saboda fadan da ake yi a tsakanin magoya bayan shugaban kasa Silvaa Kiir da mataimakinsa Riek Machar ya tilastawa mutane kusan 300,000 su ka yi hijira.
Shi dai mataimakin shugaban kasar ta Sudan Ta Kudu, Riek Machar ana yi masa shari’a bisa zarginsa da aikata laifuka akan bil’adama.
Hukumar kare hakkin bil’adama ta fitar da bayanin da yake cewa: Ana ci gaba da yin fadace-fadace a cikin yankuna da yawa, ba tare da an daina ba, tun daga rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu a 2017, tare da kara da cewa; A cikin wannan shekarar ta 2025 kadai mutane 300,000 ne su ka fice daga cikin kasar.
A tsakanin wannan adadin da akwai mutane 148,000 da su ka isa kasar Sudan, sai kuma wasu 50,000 da su ka shiga kasar Habasha. Har ila yau, wani adadin na mutane 50,000 sun isa Uganda, yayin da wasu 30,000 suka shiga kasar DRC, sai kuma 25,000 a kasar Kenya.
A cikin gida kuwa adadin mutanen da sun kai rabin miliyan ne su ka fice daga gidajensu zuwa inda za su sami tsaro.
A wani rahoto na MDD a karshen watan Yuli, ta bayyana cewa; yakin basasar kasar ta Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1800 a tsakanin watan Janairu na wannan shekara zuwa Satumba da ya shude.