Mayakan Huthi Sun Kara Kai Wasu Hare-Hare da Makamai Masu Linzami Kan BenGurio

Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic.

Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu ci gaba da kai wadan nan hare-hare har zuwa dakatar da kissan kiyashin Falasdinawa a Gaza.

Yahyah Saria kakakin sojojin kasar ta Yemen sun bayyana cewa, sojojinsa sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistic maim  suna Zulfikar wanda kuma ya fadi a kan tashar jiragen saman na Lod Airport kusa da Yafa ko tel’aviv.

Ya ce makamin ya sami bararsa kuma ya sa aka tada jiniyar hatsari a garuruwa 300 a yankin. Banda haka yace miliyoyin yahudawa ne suka je karkashin kasa don tsira da ransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted